A ranar jiya aka rufe bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na 8, inda aka cimma yarjejeniyoyin ciniki da aka kiyasta kudinsu ya kai dala biliyan 83.49 a cikin shekara guda, adadin da ya karu da kashi 4.4 cikin 100 idan aka kwatanta da na bikin bara, wanda ya zama mafi girma a tarihi. Don fadada bude kasuwa ga kasashe mafi karancin ci gaba, bikin na wannan karo ya kara fadada sassan da ke baje kolin kayayyakin Afirka, don tallafawa kasashen Afirka dake da huldar diflomasiyya da Sin wajen amfani da manufar cire haraji akan dukannin kayayyakinsu da suke fitarwa zuwa kasar Sin, har ma adadin kamfanonin Afirka da suka halarci bikin ya karu da kashi 80 cikin 100 idan aka kwatanta da na bara.
Rwanda kasa ce mai yawan noman barkono, amma saboda karancin bukatu a cikin gidanta, barkonon Rwanda ya taba fuskantar matsalar rashin samun kasuwanni. A CIIE karo na farko, miyar barkono ta Rwanda ta samu matukar karbuwa a kasuwar Sin saboda dandanonta na musamman. A watan Maris na 2021, gwamnatocin Sin da Rwanda sun sanya hannu kan yarjejeniya game da busasshen barkono na Rwanda da ake shigowa da su Sin, inda Rwanda ta zama kasar Afirka ta farko da ta fara fitar da busasshen barkono zuwa Sin. Bisa ga yarjejeniyar, kafin shekara ta 2026, masu sayar da barkono na Rwanda za su fitar da tan 50,000 na busasshen barkono zuwa Sin. A yau, noman barkono ya zama muhimmiyar sana’ar samar da kudi a Rwanda, kuma ya haifar da bunkasuwar sana’o’i masu alaka, lamarin da ya samar da karin ayyukan yi ga mutanen yankin. Jakadan Rwanda a Sin James Kimonyo ya ce, “CIIE ya zama dandali mai muhimmanci ga Rwanda don baje kolin ingantattun kayayyakinta. Za mu ci gaba da baje kolin kayayyakinmu iri-iri, mu yi amfani da wadannan budaddun dandamali, mu fitar da karin ingantattun kayayyakin Rwanda zuwa kasuwar Sin.”
Daga daukar akwati don gabatar da kayayyaki, zuwa yanzu da ake fitar da kayayyaki ta hanyar kwantena, kasashen Afirka kamar Rwanda sun samu damar habaka cinikinsu ta hanyar nuna ingantattun kayayyakinsu na noma a wannan budadden dandali wato CIIE.
Mun yi imanin cewa a nan gaba, karin kamfanonin Afirka za su ga fa’idar budaddiyyar kasuwar Sin ta CIIE, za su kuma kara zurfafa hadin gwiwa tare da Sin, da yin amfani da damammakin CIIE don samun moriyar juna. (Mai zane da rubutu: MINA)














