A wani taron manema labarai da aka saba yi yau Talata 11 ga wata, Lin Jian, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya nuna cewa bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin daga kasashen waje (CIIE), ya zama wata gada da take sada tattalin arzikin kasar Sin da kuma tattalin arzikin duniya. Yana mai cewa, “Saurin ci gaban CIIE” da “kirkire-kirkiren CIIE” sun samar da “damammakin CIIE” ga duniya, wanda hakan ya haifar da karuwar kasashe da ke shiga abin da ya yi wa lakabi da “jirgin kasa mai sauri na CIIE”.
Lin Jian ya gabatar da cewa, a wannan shekarar, kasashe da yankuna da kungiyoyi na kasa da kasa 155, da kamfanoni 290 wadanda suke cikin manyan kamfanoni guda 500 da ke kan gaba a duniya da kuma wadanda suke kan gaba a sana’o’i, sun halarci bikin baje kolin na CIIE.
Kazalika, ya ce, adadin kamfanonin da suka halarci bikin baje kolin ya karu da sama da guda 600 idan aka kwatanta da na bara, kuma fadin dandalin baje kolin da jimillar kamfanonin da suka halarta sun kai wani sabon mataki na koli.
Har ila yau, jami’in ya ce, kamfanonin kasashen duniya sun kawo jimillar sabbin kayayyaki da sabbin fasahohi da sabbin ayyuka 461, wadanda daga cikinsu akwai fiye da 200 da a karon farko ke nan aka nuna su a bainar jama’a a duniya. Bugu da kari, adadin hada-hadar cinikayyar da aka kuduri samu a bisa mizanin shekara-shekara ya zarce dalar Amurka biliyan 83.4. Sannu a hankali, babbar kasuwar kasar Sin na zama wurin gwaji, da dandalin samun riba da kuma zama filin gudanar da harkokin hadin gwiwa mai bude kofa da kuma sabbin kirkire-kirkire a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














