Baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na bakwai, da za a gudanar daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba, shaida ce na amincewa da karuwar karfin tattalin arzikin kasar Sin, da muhimmiyar rawar da take takawa wajen raya dukkan fannonin tattalin arzikin duniya tun daga hada-hadar hajojin gargajiya zuwa sabbin fasahohin da suka kasance ginshikin ci gaban tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba.
Yadda shugabannin kasashen waje da dama suka bayyana ra’ayin halartar bikin bude baje kolin da ma yadda masu baje koli daga kasashen waje suka nemi damar samun sararin baje hajojinsu, wata shaida ce ta bunkasar dangantakar cinikayya, da ta tabbatar da kasar Sin a matsayin kasuwa mai girma. Hakazalika, kasashen Norway, Slovakia, Benin, Burundi da Madagaskar, da kuma asusun bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, za su halarci baje kolin na CIIE a karo na farko, wannan ya kara tabbatar da muhimmancin da kasuwar kasar Sin ke da shi ga tattalin arzikin duniya.
- An Bukaci Amurka Da Ta Inganta Hadin Gwiwa Da Kasar Sin Kan AI
- Dalilin Da Yasa Kaduna Ke Kan Gaba A Samar Da Kuɗaɗen Shiga A Arewa – Shugaban KADIRS
Kana kasashen ketare sun kuduri aniyar nuna yadda suke cudanya da kasar Sin, da kuma yadda Sin ke da muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikinsu da kudurin fadada bunkasa tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba. Da a ce kasar Sin ba ta shiga sha’anin tattalin arzikin duniya ana damawa da ita ba, to da wadatar cinikayya tsakanin kasa da kasa ta fuskanci barazana. Kuma kamar yadda sunan ya tabbatar, babban makasudin baje kolin CIIE shi ne ya zama wurin tuntuba ga kamfanonin da ke da sha’awar kara mu’amalar cinikayya da kasar Sin, da kuma samun abokan huldar kasuwanci na kasar Sin da ke son shigo da kayayyaki ko hidimomi.
Ta hanyar turjewa takunkumi da sauran manufofin kasashen yammacin duniya da ke inganta kariyar cinikayya, baje kolin CIIE ya kasance kofar da duniya ke bi wajen shiga kasar Sin, saboda masu baje kolin sun san cewa, ci gaban tattalin arzikin duniya ya ta’allaka ne ga yin cinikayya cikin ‘yanci tare da kasar Sin. (Mohammed Yahaya)