A ranar 30 ga watan Yunin 2022 ne Mai Martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu (CFR) ke cika shekara goma sha biyu (12) a bisa karagar mulkin Masarautar Bauchi mai cike da dimbin albarka.
A shekara 12 din nan, Sarkin ya cimma dimbin nasarori wajen shimfida mulki abin koyi. Dakta Rilwanu, Sarki na 11 da Masarautar Bauchi ta yi, shi ne Sarkin Yakin Daular Usmaniyya. An samu habakar zaman lafiya, ci gaban tattalin arziki, hadin kai da dinkewar baraka a karkashinsa zmaninsa sune kuma suka kara masa martaba da kima a idon al’ummar masarautar da ma kasa baki daya.
Gwamnan Jihar Bauchi a wancan lokacin Malam Isa Yuguda ya nada Sarki Rilwanu a matsayin Sarkin Bauchi na 11 a shekarar 2010 bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Sulaiman Adamu. Gwamnan ya zabi Dakta Rilwanu ne a cikin ‘ya’yan sarki 20 da suka nemi wannan kujerar.
Dakta Rilwanu dai ya kasance daya daga cikin ‘ya’ya 16 na marigayi tsohon Sarki Alhaji Sulaiman Adamu.
Dakta Rilwanu ya kasance jajirtaccen sarki da ya damu da zaman lafiya, kwanciyar hankali, ci gaban al’ummarsa, hada kansu da kuma nuna kauna da soyayya ga kowanne bangare. Tabbas Sarki Rilwanu ya samu gagarumar nasara ta kafa tarihin gudanar da shugabanci mai cike da gaskiya, adalci, tausayi, taimako, da bai wa kowa girma daidai da yadda Allah ya ba shi.
Tabbas, duk da halin da kasar nan ke ciki a ‘yan shekarun nan, Sarkin tare da masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnatin jihar da sauran malamai da fastoci suna maida hankali wajen gudanar da addu’o’i da rokon Allah ya kare Jihar Bauchi daga kowace irin tashin hankali da fitintinu, wanda kuma hakan na haifar da da mai ido ga mazauna jihar.
Bayanai daban-daban da suke fitowa daga masarautar Bauchi na nuna cewa sarkin na daukar nauyin bayar da sadaka dukka domin neman dafawar Allah kan kyautata tsaro.
Wabin da tarihin masarautar Bauchi da Jihar Bauchi ba za su taba mancewa da Sarki Rilwanu ba, shi ne yadda yake amfani da hikima, basira, fikira, dabara, ilimi da kaifin kwakwalwa da Allah ya hore masa wajen tafiyar da kowa da kowa cikin kima da mutunci. Hatta al’ummar Kirista sun shaidi cewa Sarkin na nuna musu kauna.
Wani karin tagomashin Sarkin shi ne yadda yake iya tafiyar da kowace kungiya misali a cikin kungiyoyin addinin musulunci babu wata kungiya da ta taba jin Sarkin na nuna mata wariya.
A kowanne lokaci yana kokari wajen ganin an tafi da kowa, dukkanin manyan kungiyoyin da suka kunshi Darika, Izala, da Shi’a suna bayyana shaidarsu ta kwarai ga Sarki.
Wannan kokarin nasa bai ma tsaya kan kungiyoyin addini na musulmai da kirista ba, hatta a bangaren al’adu da ake da su, sarkin na kokarin bai wa kowa kimarsa daidai gwargwado.
Sarki Rilwanu ya kasance mai kyauta da alkairi domin kuwa lokaci bayan lokaci yana tara mabukata ya musu goma ta arziki, kana a ranar Juma’a yakan raba sadaka ga mabukata, kazalika a irin lokuta na Azumi yana ciyar da masu kananan karfi da sauran lokutan da jama’a ke cikin hali na bukata. Ya jagoranci kwamitoci daban-daban na neman yadda za a kyautata rayuwar jama’ar jihar baki daya.
Baya ga wadannan, Sarkin ya kasance a duk lokacin da ya samu baki walau ‘yan siyasa ne ko kungiyoyi a kullum maganarsa shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali, yana yawan jawo hankalin jama’a da su zauna da junansu lafiya.
Kan bunkasar zaman lafiya da ake samu a jihar Bauchi, LEADERSHIP HAUSA ta taba zantawa da Sarkin Bauchi kan sirrin da ke cikin wannan fannin inda ya amsa da cewa, “Ba abin da zan ce sai godiya wa Allah da addu’ar sakamako wa kowa da kowa. Muna kara addu’a da fatan alheri wa daukacin jama’ar da take cikin jihar Bauchi, dama wajen ta bisa goyon baya da ake bamu. Wanda yake yin sana’a kowace iri ce, Allah ya kara albarka wa abinda yake yi”.
“Ma’aikata da ‘yan kasuwa Allah ya kara masu albarka, ‘yan-makaranta Allah ya kara masu albarka, matasan mu a kullum muna addu’ar Allah ya basu yadda za a yi, abubuwa da suke damun al’umma, Allah ya kawo karshen su”.
Sarkin Bauchi ya kuma danganta zaman lafiya da walwala da a halin yanzu jama’ar masarautarsa ke ciki da ikon Allah, domin kamar yadda yace “Bamu da wata dabara sai ta Allah”.
“Bahaushe ya ce idan ka ga gemun dan’uwanka ya kama da wuta, kai ko ka shafawa naka ruwa, muna sane da ire-iren abubuwa da suke faruwa a tsakanin jama’a, wasu mun ji, wasu mun gani, idan muka auna, ba mu da wata dabara da ta wuce komawa ga Allah. Ba mu da wani hanzari face Allah shi ne madogara”.
Sarki ya cigaba da cewar, “Bayan haka sai Allah ya taimake mu kan lamuran tsaro, lamarin da ya shafi kowa-da-kowa, har kai kanka da muke magana da kai, akwai rawar da za ka taka, to sai muka bayar da dama wa kowa, Musulmi da Kirista, babba da yaro, mace da namiji, kowa yake da shawara ya kawo, duk shawara komai dacinta ba a watsi da ita, musamman ta fannin tsaro.
Muna zaune a nan za a zo a ce, Mai Martaba, kaza ga yadda za a yi shi, mu ce mun gode. Da muna kin shawarwari, kamar yadda na zayyana maku a can baya da ba haka ba, duk da cewar Allah shi ne madogara, Allah ya kawo karshen wannan matsala ta tsaro a jihar mu, shiyyar mu, kasar mu, da daukacin doron kasa bakin daya, Allah ya sa mu zama lafiya, amin. Mun gode”.
Daga nan, Sarki Rilwanu Adamu, ya gode da jinjina ga irin gudunmawa da rawar da al’umma suke takawa wajen baiwa masarautar hadin kai musamman a fannin zaman lafiya da zamantakewa, Sarkin na Bauchi yana kuma gode wa daukacin ma’aikatan gwamnati na ma’aikatu da sassa dabam-dabam na gwamnati bisa goyon baya da karfafa gwiwa da suke ba shi wajen tafiyar da jagorancin al’ummar masarautar.
Gwamnan Bala Muhammad Abdulkadir ya yaba matuka wa Sarkin na Bauchi, tare da bayyana cewar, jagoranci da iya shugabancinsa sun kasance turbar shimfida zaman lafiya tsakanin al’ummu dabam-daban na jihar Bauchi.
Sanata Bala Abdulkadir ya fahimci cewar, Sarkin Bauchi a matsayinsa na shugaban majalisar sarakuna ta jihar, ya kasance jakada na wanzar da zaman lafiya ta hanyar bayar da shawarwari da gudummawar da yake bayarwa ta yau-da-kullum wajen dorewar ci gaban jihar.
Gwamnan, wanda shi ma dan masarautar Duguri ne, ya lakanci gudummawar da sarakuna ke bayarwa wajen karfafa zaman lafiya tsakanin jama’a, yana mai cewar, a matsayinsu na ginshikan al’adu da zamantakewar jama’a, sarakuna suna taimakawa matuka wajen cimma manufofin gwamnati.
Gwamnan ya bayar da tabbacin cewar, gwamnatinsa za ta cigaba da martaba masarautun gargajiya na jihar Bauchi, hadi da martaba darajojinsu, mutumtawa da basu goyon baya da ya dace domin gudanar da ayyukansu ba tare da yi masu katsalandan ba.
Su ma da suke tsokaci kan cika shekara goma akan karagar mulki na Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Suleiman adamu, ‘ya’yan majalisar dokoki ta jihar Bauchi, sun taya Sarkin murna da wannan dama da Allah ya ba shi na jagorancin masarautar Bauchi yar zuwa yanzu.
Da yake magana a madadin ‘yan Majalisar Dokoki na Jihar Bauchi, shugaban majalisar, Rt. Hon. Abubakar Yakubu Suleiman, ya yaba wa sarkin bisa kokarinsa na wanzar da zaman lafiya, taimaka wa bunkasa tattalin arziki da ci gaban jihar.
Da ya ke zantawa da LEADERSHIP Hausa kan cikar Sarkin Bauchi shekaru 12 a mulki, Galadiman Bauchi, Alhaji Ibrahim Sa’idu Jahun, ya bayyana cewar sun koyi muhimman abubuwan daga wajen Sarkin a cikin shekaru 12 inda ya nuna cewa an samu bunkasar zaman lafiya da kwanciyar hankali a karkashin jagorancinsa.
A cewarsa: “Muna godiya wa Allah da ya kawomu yau da Mai Martaba ke cika shekara 12 a karamar mulkin masarautar Bauchi. Kamar yadda aka sani duk shugaba yana sha’awar a shugabancin da yake yi wa al’umma ya zama al’umma su na cikin zaman lafiya, tabbas mun shaidi Sarki na kokari wajen kyautata zaman lafiya.
“Sarki mutum ne mai fara’a da son al’ummarsa a kowani lokaci, yawanci in ka ga hankalinsa ya tashi ko ransa ya baci to abu biyu ne yake damunsa na farko shi ne a ga Shugabanni su na musguna wa na kasa da su ko su na cin zalinsu, in har ya ji wannan to gaskiya dole ka ga bacin ransa. Sarki mutum ne mai son zaman lafiya kuma ba ya son ya ga ana zalumci.
“Abu na biyu kuma da yake bata masa rai shine ya ga mutum yana wasa da aikinsa ko Hakimi ga abun da ya kamata ya yi bai yi ba ko Mai Gunduma ga abun da ya kamata ya yi bai yi ba to wannan ma yana bata masa rai sosai, a kowani lokaci yana son kowa ya yi aikin da aka ba shi kuma ya tabbata ya yi daidai karfinsa.
A duk lokacin da al’ummarsa suka kasance cikin zaman lafiya to Mai Martaba ya kan kasance cikin farin ciki da annashuwa.”
Galadiman na Bauchi ya kara da cewa, “An samu cigaba da yawan gaske babba shine maganar zaman lafiya tabbas Sarki ya cancanci yabo ta fuskacin wanzar da zaman lafiya sannan an samu karuwar jama’a da suka zo masarautar Bauchi domin zaman lafiyar da ake more.
Bisa kokarinsa, hikima da basirarsa Gwamnatin tarayya ta ga ya dace ta ba shi shugabancin jami’ar Abuja.”
“A kullum Sarki yana yawan nanata maganar sana’a yana yawan kiran matasa da cewa su nemi sana’ar yi, maganar zaman banza ba nasu ba ne a kowani lokaci yana nuna rashin jin dadinsa idan ya ga yara su na zaman banza, abun da yake fadakarwa kuma yake so shine in yaro baya karatu to yana sana’a, in aka samu abun yi hakan ne zai sanya jama’a su kara samun cigaba mai daurewa.”
Alhaji Ibrahim Sa’idu Jahun ya jinjija wa al’ummar masarautar Bauchi a bisa hadin kai da goyon bayan da suke bai wa Sarkin na Bauchi inda ya bukacesu da su kara himma wajen bada hadin kai da koyi da dabi’un zaman lafiya domin kyautata a zamantakewa a kowani lokaci.
Sai ya ce sirrin da ake da shi na zaman lafiya a masarautar Bauchi da jihar Baki daya ma shine yawan rokon Allah da wanzar da adalci a kowani lokaci, “Addu’a ne muka sanya a gaba kuma shi Mai Martaba a kullum ya kan nanata bukatar a yi ta addu’a domin daurewar zaman lafiya. Sai Kuma adalci, wanzar fa adalci a tsakanin jama’a yana bunkasa zaman lafiya a tsakanin al’umma.”
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa kan cikar Sarkin Bauchi shekaru 12 a karagar mulki, Amb. Nazeeb Sulayman Ibraheem, Jikan Gidan Sarakin Bauchi ya bayyana cewa, “Duk da shekarunsa basu dara 40 a lokacin da Allah ya ba shi sarautar Bauchin Yakubu ba, halayyarsa na kirki ne, sai godiya ga Sarki Allah.
“Dr. Rilwanu Sulaimanu Adamu matashi ne mai farin jinin jama’a. Ya kasance mai da’a da karimci. Zamansa sarki ya kara masa soyuwa a zukatun ‘ya’yan Bauchi da sauran kabilu mazauna cikinta.”
“Kamar yadda mahaifinsa yake a lokacin rayuwarsa mai kyautata wa talakawansa, makwabta, ‘yan uwa da baki, haka Dr. Rilwanu Sulaimanu Adamu ya kasance. Babu abinda ya rage daga halin ‘yan baya.
Hasali ma, Sarkin adalci ya tafi ne, sarkin adalci ya maye gurbinsa.”
Ya kara da cewa, “Kamar mahaifinsa, Sarki Rilwanu mai saukin kai ne. Kowa nasa ne.
Kowa na zuwa gabansa – babba ko karami, talaka da attajiri, dan gida ko bako. An san shi da haba-haba da jama’a da karbar baki babu nuna bambanci.”
“A mulkinsa na shekaru 12 ya-zuwa yau, Sarki Rilwanu Sulaimanu Adamu ya nuna mulkin adalci.
Adalci a jinin Masarautar Bauchi yake. Sarki Rilwanu Sulaimanu Adamu baya goyon bayan maras gaskiya. Yana kyamatar rashin gaskiya da son zuciya. Yana shari’a ya ba wa kowa hakkinsa – ba sani, ba sabo.”
Amb. Nazeeb Sulayman ya kara da cewa, babu wanda ya taba zuwa gaban Sarki Rilwanu Sulaimanu Adamu da wata bukata ta halak ya tashi bukatarsa bata biya ba. Sarkin Bauchi mai jin kukan jama’arsa ne. Yana damuwa da damuwar jama’arsa.
“Dr. Rilwanu jagora ne na hakika. Jagorancinsa bisa amana da gaskiya yasa a shekarar 2014 aka zabe shi ‘Amirul-Hajj’ na kasa. Wannan ya nuna irin kokarinsa da jajircewarsa ne kan bukatun talakawa. Kuma ya nuna halin nagarta da bada hakkokin mahajjata a kasa mai tsarki a shekarar inda bayan an dawo gida Nijeriya gwamnatin tarayya ta ba shi takardar yabon iya jagoranci.
“Mu ‘yan Bauchi shaida ne ganin yadda Mai Martaba Sarki Rilwanu Sulaimanu Adamu ke sa ‘ya’yan makwabtan Fada a matakan makarantu dabam-dabam ya biya musu kuɗin makaranta. Wannan irin salon shugabanci abin farin ciki ne.”
Kazalika, ita ma Cibiyar Hulda Da Jama’a ta Kasa (NIPR) reshen jihar Bauchi, ta misalta mulkin Mai Martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu a matsayin shekaran da aka samu gagarumar nasara ta fuskacin kyautatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Shugaban kungiyar a Jihar Bauchi Alhaji Kabir Ali Kobi shi ne ya shaida hakan yana mai cewa bisa kokarin wanzar da adalci ga kowa ba tare da nuna banbanci ba; na daga cikin ababen da suka janwo wa Sarkin kima da martaba a idon al’umma da suke fadin Masarautar, yana mai nuna cewar Sarkin ya zama abun koyi ga jama’a.
…Tarihin Sarki Rilwanu Da Jerin Sarakunan Da Suka Mulki Bauchi A Takaice
LEADERSHIP Hausa ta nakalto cewa an haifi Dakta Rilwanu ne a ranar 14 ga watan Oktoban 1970 a garin Bauchi, ya halarci makarantar Firamare ta Kobi da ke kwaryar Bauchi a tsakanin shekarar 1976 zuwa 1982, ya kuma tafi sakandarin gwamnati da ke Toro daga shekarar 1982 zuwa 1987, daga nan kuma ya zarce zuwa kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin Jihar Bauchi wato Tatari Ali (ATAP) daga shekarar 1991 zuwa 1995 wanda ya samu shaidar ilimin malanta ta koyarwa (NCE), ya kuma zarce zuwa jami’ar ATBU da ke Bauchin domin samun shaidar digiri na farko a bangaren kimiyyar gine-gine (Bsc in building technology) daga 1996 zuwa 2001.
Mai martaba Sarkin na Bauchi ya yi aiki a tashar jiragen ruwa ta Ikko daga shekarar 2002 zuwa 2006, kafin a nada shi a matsayin sarkin Bauchi, ya kuma yi aiki a hukumar hadin kai tsakanin kasar Nijeriyya da ta Sao-Tome Da Principle.
Bisa gudunmawar da yake bayarwa a cikin al’umma, Jami’ar Crescent Abeokuta da jami’ar kimiyya ta gwamnatin tarayya da ke Akure sun nada shi a matsayin shugabansu ‘Pro-chancellor’ sai kuma gwamnatin tarayya ta nada shi a matsayin shugaban Jami’ar Abuja a kwanan baya, da sauran nade-haden da aka masa domin nuna godiya bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen cigaban al’umma a jiharsa da kasa baki daya.
Tarihi dai ya nuna cewa masarautar Bauchi ta fara yin sarki na farko wato Malam Yakubun Bauchi wanda almajirin Sheikh Usman Danfodio ne, kuma ya yi yaki sosai wajen tabbatar da addinin musuluci, ya zama sarkin Bauchi daga shekarar 1805 zuwa 1845, bayan da ya rasu ne kuma Ibrahim Dan Yakubu ya yi mulki na tsawon shekara 32 daga shekarar 1845 zuwa 1877.
Sarki na uku, Usman Dan Ibrahim shi ne ya gaje shi a tsakanin 1977 zuwa 1883, sai kuma Sarki Umaru Dan Salmanu da ya yi mulki tsakanin 1883 zuwa 1902, Muhammadu Mu’allayidi Dan Ibrahima ya zama sarki amma bai jima ba ya rasu don watanni kalilan ya yi a kan mulkin, ya rasu ne a 1902, bayan rasuwarsa Sarki Hassan Dan Mamudu ya mulki masarautar Bauchi a tsakanin 1903 zuwa 1907.
Sauran sarakunan da masarautar Bauchi ta yi sun hada da Ya’kubu II Dan Usman da ya kasance sarki na bakwai da ya yi mulki a tsakanin 1907 zuwa 1941, sai Yakubu III Dan Umaru tsakanin 1941 zuwa 1954, bayan shi sai kakan sarki mai ci a yanzu, Alhaji Adamu Jumba da ya kasance sarki na tara, inda ya yi mulki na tsawon shekara 27 a tsakanin alif 1955 zuwa 1982, sai kuma Dakta Sulaiman Adamu da ya kasance Sarki na 10 da ya mulki masarautar Bauchi tsakanin 1982 zuwa 2010, ya kuma rasu yana da shekara 77 a duniya. Sai kuma dansa Dakta Rilwanu da ya zama sarki na 11 da yake kan karaga a halin yanzu.