Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina ta sanar da kama sama da mutane 200 da ake zargi da laifuka daban-daban a fadin jihar a cikin watan Oktoba, 2025.
Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yansandan (PPRO), Sadiq Abubakar ne ya sanar da hakan, yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a hedikwatar ‘Yansandan da ke Katsina.
- Kofin Duniya 2026 Zai Zama Na Ƙarshe A Wuri Na – Ronaldo
- An Kaddamar Da Babbar Hanyar Mota Da Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa A Namibia
A cewar rundunar, an kama mutanen ne sakamakon kararraki 120 da aka kaiwa rundunar da suka shafi manyan laifuka kamar fashi da makami, kisan kai, fyade, ta’ammuli da miyagun kwayoyi, da kuma garkuwa da mutane.
An kama mutane 18 bisa laifin fashi da makami, mutane 28 bisa laifin kisan kai, mutane biyar bisa laifin yunkurin kisan kai, mutane 20 bisa laifin fyade da laifukan da ba su dace ba, da kuma mutane 28 bisa laifin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.
Jami’in ‘Yansandan, ya kara da cewa, daga cikin jimillar kararrakin 120, an gurfanar da mutane 97 a gaban kotu, yayin da ake gudanar da bincike kan 22 a halin yanzu.
Bugu da kari, an ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka yi safarar su amma tuni an hada su da iyalansu.
Jami’in ya kuma nuna wasu kayayyaki da aka kwato a hannun masu laifin da suka hada da bindiga kirar AK-47 guda daya, bindiga kirar gida guda daya, harsasai 183, motoci uku, babura uku, babur mai kafa uku (Keke-napep) daya, da kuma dabbobi sama da 200 da aka sace.














