Shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma.
Tsokacin yau zai yi magana ne akan abin da ya shafi bashi, duba da yadda wasu mutanen ke daukar bashi ba komai ba, yayin da za su ci bashin mutane kuma su ki biya da gangan, wanda hakan ke iya zamowa zumunci ya tarwatse ta dalilin bashin.
Wannan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; Ko me yake janyo cin bashi? Me ne ne amfani ko rashin amfanin cin bashi?, Wanne irin matsaloli cin bashi ke haifarwa?, Wadanne irin matsaloli ne ke sakawa a ci bashi?
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Zainab Zeey Ilyas, Jihar Kaduna:
Abin da yake janyo cin bashi shi ne; da yawan wasu mutanen ba su da godiyar Allah, suna hangen wasunsu, kamar karin maganar da Hausawa kan ce ba kada gashin wance – ka ce za ka yi kitsan wancen, wasu kuma dole ce take sakawa su ciyo bashin, misali ba suda abincin da za su ci madadin su zauna babu sai su ranto su ci, wasu kuma kamar yadda na fada fafa ce kawai, da son ace su ma wasu ne, ba suda shi amma su dage sai sun yi. Cin bashi yana zubar da kima da mutunci a idon mutane da kuma wanda aka ranci kudi, babu wani amfani a cin bashi.
Sunana Ibrahim Danmulky, Jihar Kano Karamar Hukar Nassarawa Unguwar Gama:
Abin da yake janyo cin bashi dalilai ne masu yawa amma daga ciki akwai rashin wadata bi ma’ana babu. Gaskiya idan ba dole ya zame wa mutum ba, cin bashi ba shi da wani amfani ko fa’ida ga mutum tunda ba a fiya wanyewa lafiya ba. Cin bashi yana haifar da rabuwar hankali, rashin nutsuwa, da kuma takurama kai da dai sauransu. To daga cikin abin da ke sa a ci bashi akwai rashin lafiya, rashin muhalli, rashin abincin da za a ci da sauransu. To gaskiya shawarata ita ce mutum ya zama mai wadatar zuciya, duk abin da bai zama dole ba to kar a ci bashi saboda wasu idan ka kalli cin bashin nasu ma akwai takurawa kai a ciki, sannan masu cinyewa su sani Allah ya hana Annabi ya hana su ji tsoron Allah su tuna da mutuwa.
Sunana Hafsat Sae’ed, Jihar Neja:
Ni dai a fahimtata abin da yake janyo cin bashi yana da yawa, wasu babu ne kuma ga ‘ya’ya ga laluran yau da kullum saboda yaro dole ka nemo ka basu, wasu kuma kwadayi gaskiya ke damunsu ba kada shi ka ga wata da shi sai kai ma ka yi koda kuwa bashi ne sai ka ciyo shi. Amfanin cin bashi in kana cikin yanayi na babu kuma ga iyalai kana da me baka aro dole za ka nemi aro in ka samu ka bayar, rashin amfani kuwa shi ne masu cin bashin don sun ga wata ta sa me kyau su ma sai sun saka, sai su je su ciyo bashi anan kam babu amfani. Matsalolin da cin bashi ke sawa game imanin biya shi ne rashin kwanciyar hankali. Matsalolin dake sawa a ciyo bashi suna da yawa akwai yunwa, rashin lafiya, ko a koro maka yara daga makaranta da dai sauransu. Shawarata ga masu cin bashi su rage saboda halin rayuwa, masu kin biyan bashi kuwa shawarata gare su shi ne su ji tsoron Allah su rinka biyan bashi don kuwa in mutun ya barka da hakkinshi fa akwai ranar gobe don kuwa bashi na hana kwanciyar kabari Allah ya sa mu dace.
Sunana Abbas Haruna Jihar Gombe:
Abin da yake janyo cin bashi dai wani lokacin kamawa take idan ba kada shi kuma kana da wani uzuri ko abinci da za ka ci, wanda ba kada kudi dole zai sa sai ka ci bashi. Cin bashi bai da amfani sai dai idan kana da wani abin da za ka sayar, kuma wani uzuri ya same ka na gaggawa za ka iya cin bashi daga baya idan ka sayar sai ka biya bashin da ake binka. Matsalar da cin bashi ke haifarwa shi ne duk yadda ku ke da mutum koda baya son tambayarka yana jin kunyar ka akwai lokacin da fa zai cire kunya ya nuna bacin ransa har ku samu matsala a tsakaninku. Wani lokacin kuma abin da ya sa ake cin bashi yana kamawa dole ne sanadiyar rashin babu wanda kuma idan baka ci bashin ba za ka iya shiga wani damuwa. Shawarar da zan bawa masu cin bashi ya kamata kayi tunani kuma ka ji tsoron Allah kafin ka ci bashin nan ya zamana kana da yakinin za ka samu ka bawa wanda kaa karbi kudin shi dan wasu sun maida cin bashi sana’a Allah ya taimake mu.
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Jihar Kano:
Yawanci matsin rayuwa ke sa cin bashi, wani kuma saboda ko yana da kudin siyan abu sai ya ci bashin saboda ya zame masa jiki da jini. Wani lalura ce ta sakawa wani yanayi rayuwa wani kuma dole ce,wani kuma haka kawai. Ai cin bashi ba shi da wani rana balle al fannu sai ma jawa kai matsala da ta tashin hankali a rayuwa da shiga dar-dar. Jefa rayuwa cikin halin ni ‘ya su dan wani ta haka gidan maza ake kai shi, su yi karatun ta nutsu su daina.
Sunana Sadik Abubakar, ‘Yammata Rijiyar Lemo Jihar Kano:
Bashi hanji ne, yana cikin kowa.’Wannan magana sananniya ce a bakin Hausawa, musamman wadanda suka kunna nutso cikin duniyar bashin. Wadanda suka kallafa wa kansu yin rayuwa ba tare da sun ci bashi ba. Abubuwan da ke janyo cin bashi suna da yawa, kuma sun bambanta a tsakanin mutane, wasu mutanen dalilansu na cin bashi abin a duba ne, wasu kuwa sam uzurinsu ba zai karbu ba. Tsananin bukatar wani abu ko aiwatar da shi a takaitaccen lokaci kan iya sawa a ci bashi, misali idan lalura ta samu mutum da ake bukatar kashe kudi kuma ba shi da su, to a nan mutum zai iya neman bashi ya karba domin kawar da larurar da ta taso. Amfanin cin bashi bai wuce na rufin asiri ba da kauce wa matsaloli da kan taso a dalilin babu. Matsalolin da cin bashi yake haifarwa su ma suna da yawa kamar yadda dalilan cin nasa suke da yawa. Na farko idan aka yi rashin sa’a maimakon asiri ya rufu ta dalilin cin bashin to sai dai ma ya karu. Sannan idan bashi ya zama dabi’ar mutum ya kan rage masa Æ™ima da daraja a cikin al’umma. Bashi babbar masifa ce, kamar yadda malamai suka bayyana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ki sallatar gawar da ake bi bashi har sai da aka biya.
Shawarata ga masu cin bashi shi ne, su kula sosai su yi duk mai yiyuwa wajen ganin sun kaurace wa cin bashin, idan sun yi iyakacin kokarinsu ba su samu dama, to su karba daidai gwargwado kuma da kyakkyawar niyyar biya sai Ubangiji Ya dafa musu. Allah Ya sa mu dace.
Sunana Hadiza Muhammad, Gusau Zamfara:
Gaskiya ne wannan lamari yana faruwa, wanda kuma bai dace ba. Ya danganta gaskiya, wasu matsuwa ce, yayin da wasu kuma son zuciya ce. Amfanin cin bashi, yana rufa maka asiri a lokacin da baka da halin yin abu, kuma ya kamata kuma ya zama tilas kayi shi. Rashin amfaninshi kuma yana hana kwanciyar hankali, yana kuma janyo wa wanda ke cinshi wulakanci a mafi yawan lokuta. Matsaloli da yawa, tun daga duniya har a lahira. Kadan daga ciki shi ne; yana sa wadanda ke ganin girmanka su dawo basa gani, wanda bai isa ba sai ya tozarta ka akan kaci bashinshi. Yana sa jin kunya, sannan a karshe ya hana mai cinshi kwanciyar kabari.
Babbar matsalar dake sa sai an ci bashi mafi yawanci bai wuce rashin abinci, sai kuma ciwo, amma a mahanga ta. Shawara daya ce, mutum ya tsaya inda Allah ya aje shi, a kuma ji tsoron Allah a ringa biya in an ci, dan bashi yana bin mutum lahira, ya ja mishi hasarar ayyukan shi na alkhairi.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya abubuwan dake janyo cin bashi suna da yawa, to amma akwai masu muhimmanci akwai marasa muhimmanci, kadan daga cikin masu muhimmanci akwai; rashin lafiya, neman jarin sana’a da sauransu, marasa muhimmanci kuma sune kamar; rayuwar gasa da wani da kuma neman duniya ta kowane hali. To cin bashi yana da muhimmanci muddun idan akwai dalilai kamar rashin lafiya ko neman jarin sana’a domin dogaro da kai, amma kuma bashi da amfani wajen yin koya da rayuwar gasa da wani ko kokarin neman arziki ta kowane hali, domin karshe ana karewa a da-na-sani. To farko dai akwai zubda mutunci, rashin ganin daraja ko kaskanci a wasu lokutan, kuma yana jawowa mutum rashin sukuni a rayuwar sa, har ta kai kuna wasan buya da masu dukiyar da suka baka bashin. To na farko dai akwai rashin lafiya domin dole ne ayi amfani da kudi wajen neman lafiya ka ga kuwa idan babu dole ne a nemi bashi, na biyu akwai neman jarin sana’a domin dogaro da kai, domin illar zaman banza tafi illar cin bashi a cikin Al’umma don haka wadanan dalilai suna sawa dole a nemi bashi domin gudanar da su. To da farko dai mutum ya nemi bashin da kyakkyawar manufa ko zuciya idan kuma ya samu sai yayi amfani da shi yadda ya dace domin hakan zai taimaka wajen ya samu damar biyan bashin kuma Allah zai duba zuciyar sa ya kawo masa mafita.daga nan nake addu’ar Allah ya raba mu daga karbar bashi mai nauyi wanda ba za mu iya biya ba.
Sunana Rabi’atu Abdullahi, Jihar Kano:
Bukatu idan suka yi wa mutum yawa kuma ba shi da halin yi sai ya nemi bashi. Amfanin cin bashi biyan bukata, a aiwatar da shi ta dalilin da ya sa aka ci bashin, Rashin amfanin sa; rashin aiwatar da shi ta dalilin da aka karba misali mutum ya karbi bashi dan ya ja jari ya fara sana’a kuma ya cinye kudin ba tare da ya gina sana’ar ba. Matsalolin da cin bashi ke haifar wa akwai rashin kwanciyar hankali. Abin da yake sawa dole aci bashi yunwa, rashin abinci, da karyewar arziki, kasuwanci da dai sauransu. Idan mutum ya san ba zai iya biya ba bai kamata ya karba ba sannan ka aiwatar da shi ta dalilin da ya sa ka karba da dai sauransu.
Sunana Ibrahim Isma’il Jogana, Jihar Kano:
Abin da yake jawo cin bashi wani baya dashi wani kuma abin ya bi mishi jini ko yana dashi sai ya ci bashi, yana da amfani idan ya zama ka ci shi a gabar da ya dace, rashin amfaninsa shi ne; kawai ya zama ya bi wa mutum jiki idan bai ci ba baya jin dadi matsalar da cin bashi yake jawowa na daya idan ya zamana za ka karba ka ki biya yana jawo zubar da mutunci wurin da ake ganin kiimarka a daina, idan ka dawo ma a hanaka. Akwai matsalolin da suke jawo aci bashi irin rashin lafiya ko yanayi na kana da iyali ba kada shi a lokacin baka da yadda za a yi ka samu ko yunwa dai da sauransu.
Sunana Khadija Abdullahi:
Talauci: wasu talauci ke saka su cin bashi ko rashin biyan albashi da wuri na saka cin bashi. Ko mutum ya ga abu yana so kuma ba:shi da kudi a lokacin sai ya dauka bashi idan ya samu ya biya daga baya. Anfanin cin bashi shi ne; mutum ya karbi bashin da ya san idan ya samu kudi ba zai iya siyan wannan abun ba. Amma idan ya karbi bashi ya san dole zai biya kudin wannan abun. Rashin amfanin cin bashi kuma shi ne; mutum ya zo ya rasu ba a san ana binsa bashi ba, shi ne babban alfanun son rashin cin bashi.