Alkaluman cinikayyar albarkatun gona na kasar Sin da kasashen ketare, sun karu da kaso 6.4 bisa dari a rabin farko na shekarar bana. Alkaluman kididdiga da ma’aikatar noma da raya karkara ta Sin ta fitar sun nuna cewa, a tsakanin wannan wa’adi, darajar albarkatun gona da Sin ta shigo da su daga ketare, da wadanda ta fitar sun kai dalar Amurka biliyan 171.76.
Kaza lika, adadin albarkatun gona da Sin din ta fitar ya karu da kaso 1.7 bisa dari a shekara, inda darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 47.71. A hannu guda kuma, adadin wadanda ta shigo da su ya kai na dala biliyan 124.05, adadin da shi ma ya karu da kaso 8.3 bisa dari idan an kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Bugu da kari, rarar cinikayyar albarkatun gona da Sin din ta samu a watannin 6, inda ya kai dala biliyan 76.34, adadin da ya karu da kaso 12.9 bisa dari a shekara guda. (Saminu Alhassan)