Alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna yadda cikin watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2025, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta kasar Sin ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.5, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 3.5 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar bara. Daga cikin adadin, darajar mizanin fitar da kayayyaki ya kai yuan tiriliyan 15.31, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.1, adadin da ya karu da kashi 7.3 cikin 100, yayin da mizanin shigo da kayayyaki shi ma ya kai yuan tiriliyan 10.39, kwatankwacin dalar Amurka triliya 1.44, adadin da ya ragu da kashi 1.6 cikin 100.
A watan Yuli, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta Sin ta kai yuan tiriliyan 3.91 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 544, adadin da ya karu da kashi 6.7 cikin 100. Daga wannan adadi, mizanin fitar da kayayyaki ya kai yuan tiriliyan 2.31, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 321, inda ya karu da kashi 8 cikin 100. Sai kuma mizanin shigo da kayayyaki da ya kai darajar yuan tiriliyan 1.6, kwatankwacin dala biliyan 222, wanda shi ma ya karu da kashi 4.8 cikin 100, wanda hakan ke nuna ci gaba da karuwarsa a tsawon watanni biyu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp