Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin MOFCOM, ta ce tun daga farkon shekarar nan ta bana, Sin ke ta samun bunkasar hada hadar kasuwanci, inda ta cimma nasarar ci gaba mai inganci, ta kuma kara bayar da gudummawa mai karko ga ci gaban tattalin arzikin kasa.
Da take bayyana hakan, yayin taron manema labarai na Juma’ar nan, mataimakiyar babbar mai shawarwari na Sin a fannin hada hadar cinikayyar kasa da kasa Li Yongsha, ta jaddada cewa, yawan sayayya a kasar Sin na ci gaba da fadada bisa daidaito, inda darajar jimillar sayayyar daidaikun hajojin a kasar ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 23.6, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.3 a farkon rabin shekarar bana, karuwar da ta kai ta kaso 3.7 bisa dari a shekara.
Jami’ar ta ce cinikayyar waje ta Sin ma ta ci gaba da bunkasa, yayin da hada hadar shige da ficen hajoji ta karu da kaso 6.1, kana fannin samar da hidimomi ya karu da kaso 14 bisa dari a rabin farko na shekarar ta 2024, wanda hakan ya samar da gudummawar kaso 13.9 bisa dari ga bunkasar tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp