Hukumar kwastan ta kasar Sin, ta ce hada-hadar cinikayyar waje ta Sin ta karu da kaso 4.8 bisa dari a rubu’in farko na shekarar 2023 da muke ciki, idan an kwatanta da na shekarar bara, inda darajar cinikayyar wajen ta kai yuan tiriliyan 9.89, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.44, kuma cinikayyar kasar na ta kara bunkasa tun daga watan Fabarairu.
Alkaluman da hukumar ta fitar a Alhamis din nan, sun ce a wa’adin watanni 3 na farkon shekarar nan, mizanin hajojin da Sin ta fitar ya karu da kaso 8.4 bisa dari, inda darajar sa ta kai kudin kasar tiriliyan 5.65, yayin da na hajojin da ake shugowa da su kasar ya karu da kaso 0.2 bisa dari, wato darajar kimanin yuan tirliyan 4.24.
A cewar kakakin hukumar Lyu Daliang, yanayin da ake ciki yanzu, na koma bayan bukatun hajojin Sin daga waje, wanda hauhawar farashin kayayyaki na duniya, da tafiyar hawainiya ta fuskar tattalin arziki da manyan kasashen duniya suka fuskanta, ya yi matukar tasiri ga cinikayyar waje ta Sin.
To sai dai kuma sakamakon bunkasar tattalin arzikin da Sin ke samu, ana hasashen fadadar cinikayyar waje ta Sin, za ta ci gaba da karuwa. Kaza lika cinikayyar kasar da kasashen nahiyar Afirka, ta karu da kaso 14.1 bisa dari a rubu’in farko na shekarar ta bana. (Saminu Alhassan)