Babbar hukumar kwastom ta kasar Sin GAC, ta sanar da cewa, a watanni biyar din farko na shekarar 2022, hada-hadar cinikayyar kasashen waje na kasar Sin ya samu karin kashi 8.3 bisa 100, idan an kwatanta da makamancin lokacin bara inda adadin ya karu zuwa RMB yuan triliyan 16.04.
Ta fannin dalar Amurka kuwa, jimillar cinikayyar kasashen wajen ya kai dala triliyan 2.51 a cikin watannin biyar, inda ya karu da kashi 10.3 a bisa na makamancin lokacin bara.
A cikin wannan wa’adi, cinikyyar kasar Sin da manyan abokan huldar kasuwanci uku, wato kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya, da kungiyar tarayyar Turai, da kuma Amurka, ya karu da kashi 8.1 bisa 100, da kashi 7 bisa 100, da kuma kashi 10.1 bisa 100, idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.
Daga watan Janairu zuwa Mayu, huldar kasuwancin Sin da kasashen dake bin shawarar “ziri daya da hanya daya”, ya karu zuwa kashi 16.8 bisa 100 a bisa na makamancin lokacin bara, inda ya karu zuwa RMB yuan triliyan 5.11.
An samu farfadowar ne bayan da gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan tallafawa kamfanonin kasashen ketare, wajen rage musu wahalhalu a sakamakon barkewar annobar COVID-19 a cikin gida, da kuma rashin tabbas a yanayin kasashen ketare.
Li Kuiwen, jami’in babbar hukumar GAC, ya bayyana cewa, kasar Sin ta bullo da wasu jerin matakan daidaita yanayin tattalin arziki, da kuma inganta yanayin kasuwancin waje a cikin wannan shekarar, matakan wadanda dama an yi tsammanin za su taimaka wajen saurin farfadowar tattalin arzikin da zarar suka fara aiki. (Mai Fassarawa: Ahmad Fagam)