• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ciniki Tsakanin Sin Da Kasashen Waje Na Samun Bunkasuwa Yadda Ya Kamata

byCGTN Hausa
1 year ago
Sin

Alkaluman da kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Mayun bana, darajar cinikin shige da fice na kasar ta kai kudin Sin Yuan triliyan 17.5, kwatankwacin fiye da dalar Amurka biliyan 2413.5, wanda ya karu da 6.3% bisa makamancin lokacin bara. Abin lura shi ne, saurin bunkasuwar cinikin shige da fice a watan Mayu ya kai 8.6%, wanda ya karu da 0.6% bisa na watan Afrilu. Kafofin yada labaran kasashen waje, ciki hadda Reuters sun nuna cewa, cinikin da Sin take yi da kasashen waje na samun ci gaba fiye da hasashen da aka yi, duk da shingayen da Amurka da wasu kasashen Turai suka sanyawa kasar, lamarin dake bayyana cewa, kamfanonin Sin sun cimma nasarar habaka kasuwannin ketare, kana tattalin arzikin kasar Sin na da karfin juriya.

Hakika dai, ba hajoji kawai kasar Sin take sanarwa duniya ba, ta kuma gabatarwa duk duniya sabbin damarmaki da babbar kasuwa. Alkaluma na nuna cewa, a cikin watanni 5 na farkon bana, yawan hajojin da Sin ta shigo da su ya karu da 6.4% bisa na makamancin lokacin a bara, tana kara shigo da kayayyaki masu yawa.

A kwanakin baya, asusun ba da lamuni na duniya wato IMF da bankin Paris na kasar Faransa da bankin Amurka da sauran hukumomin hada-hadar kudi a duniya, sun kyautata hasashensu kan bunkasar tattalin arzikin Sin zuwa 5%, saboda yadda ciniki ke samun bunkasuwa tsakanin Sin da kasashen ketare. Kafofin yada labarai na duniya da dama sun nuna cewa, a kasar Sin, GDPn mai yawa da kyakkyawan tsare-tsaren masana’antu, da karuwar yawan mutane masu matsakaicin kudin shiga, sun zama abubuwan da masu zuba jari na kasashen waje ba za su yi watsi da su ba, kuma Sin jigo ne mafi girma na ci gaban tattalin arzikin duniya. (Amina Xu)

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Me Ya Sa Shirin EU Na Kakaba Karin Haraji Kan Motoci Masu Amfani Da Lantarki Kirar Sin Bai Samu Karbuwa Ba?

Me Ya Sa Shirin EU Na Kakaba Karin Haraji Kan Motoci Masu Amfani Da Lantarki Kirar Sin Bai Samu Karbuwa Ba?

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version