Kwanan baya, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da alkaluma game manyan kasashe da suka yi shige da ficen kayayyaki a watan Yulin 2024 a shafinta na intanet. Bisa alkaluman, daga watan Janairu zuwa watan Yulin bana, yawan kudin kayayyakin shige da fice da Sin ta yi cinikayyar su tare da kasashen nahiyar Afirka ya kai yuan biliyan 1188.82.
Shugaban sashen nazari na babbar hukumar ta kwastam Lv Daliang ya bayyana cewa, a watanni bakwai na farkon shekarar bana, adadin cinikayyar hajojin da ba a gama sarrafa su ba da Sin ta yi da kasashen Afirka ya karu da kashi 6.4 cikin dari, wanda ya kai kashi 68 cikin dari, na jimilar yawan kudin kayayyakin shige da fice tsakanin Sin da Afirka, lamarin da ya shaida cinikayyar Sin da Afirka na inganta ci gaban masan’antu, da tattalin arzikin Afirka.
Lv Daliang ya kara da cewa, za a gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na 2024 a Beijing, kuma ana sa ran za a zurfafa hadin gwiwar cinikayya, da tattalin arzikin bangarorin biyu bisa wannan dama.(Safiyah Ma)