Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada umurnin gaggauta raba kayan abinci a ƙananan hukumomi 14 dake faɗin Jihar domin rage raɗaɗin wahalar da janye tallafin fetur ya jefa al’umma.
Wata sanarwa wacce mai magana da yawun gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa za a yi rabon wannan kayan abinci ne duba da irin mawuyacin halin da al’umma ke ciki, kuma bisa ƙudurin gwamnatin Jihar na bin duk wata hanya ta sauƙaƙawa jama’a.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin ta yi shiri mai kyau don tabbatar da cewa mabuƙata sun amfana da wannan tallafi.
Ya ce: “Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bada umurnin a gaggauta raba kayan abinci ga al’umma a matsayin agajin gaggawa don rage raɗaɗin halin da ake ciki sakamakon janye tallafin mai.
“Ɓangare na farko na wannan tallafi zai fara da rabon Shinkafa da Masara.
“Tuni dai an samar da hanyoyin yin wannan rabo sannan kuma an kafa kwamitin da zai ɗauki alhakin wannan aiki.
“Bugu da kari, gwamnatin ta Zamfara ta yi amanna cewa wannan tallafin na kayan abinci zai amfani al’umma, kafin sauran tallafin su biyo baya.”