Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa (CITAD) da tallafin kungiyar ci gaban sadarwa (APC) ta horas da matasa 40 a jihar Kano kan kwarewa a bangaren gyaran fasaha da sake amfana (3R).
Kazalika, shirin na da manufar shawo kan barazanar lafiya ta hanyar amfani da fasaha wajen maida abubuwan da suka kasance marasa amfani zuwa yadda za a sake amfani da su domin ci gaba. Da ya ke jawabi a wajen horon a ofishin CITAD da ke Kano, Malam Ibrahim Nuhu, wanda ya wakilci babban daraktan CITAD Mr. Y.Z. Ya’u, ya bayyana alfanun da matasan za su samu a yayin horon da cewa na da gayar fa’ida a garesu.
- Gwamnatin Kano Za Ta Biya Wadanda Ta Yi Wa Rusau Diyyar N3bn
- Gwamnati Ta Dakatar Da Daraktocin Hukumar Sufurin Jiragen Sama 5 Sa’o’i Kadan Bayan Sauke Shugabanninsu
Ya yi kira ga masu samun horon da su tsara daftarin kasuwanci na shekara 15-20 gami da jaddada muhimmancin yin rijista da hukumar kula da kamfanoni CAC domin kyautata aiki.
Nuhu ya ce, babbar manufar shirin shi ne yadda za a daura matakan kan yadda za su kasance masu iya amfani da zamani wajen maida abubuwan da suka kasance marasa amfani zuwa ga yadda za su yi amfani domin bunkasa tattalin arziki.
Ya ce, rungumar yadda za a sake sauya kayan lankarki zuwa ga sake amfani da su zai taimaka wajen kyautata kiwon lafiya, samar da damarmakin bunkasa abubuwan ayyukan yi a tsakanin jama’a da matasa, da kuma taimaka wajen kyautata harkokin tattalin arzikin kasa.