A yau ne, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da hukumar kwallon kafar kasar Afirka ta Kudu suka yi musayar yarjejeniyar hadin gwiwa a birnin Johannesburg. Sassan biyu sun cimma matsaya kan karfafa yin mu’amala ta fuskar al’adun kwallon kafa da wasanni, watsa shirye-shirye kan wasanni da yin hadin gwiwa, da kaiwa juna ziyara tsakanin ma’aikatan sassan biyu
Bisa yarjejeniyar hadin gwiwar, bangarorin biyu za su karfafa hadin gwiwar al’adun kwallon kafa a tsakanin kasashen biyu, da sa kaimi ga yin wasannin kwallon kafa tsakanin kungiyoyin kasashen biyu, da samar da yanayin da ya dace na tsara da watsa shirye-shirye kan wasanni, da kuma karfafa musayar ma’aikata da jami’ai. (Ibrahim)