An kammala gasar fada tsakanin mutum-mutumin inji cikin jerin gasannin mutum-mutumin inji ta kasa da kasa a ran 25 ga watan nan da muke ciki a birnin Hangzhou dake gabashin kasar Sin. Gasar ta fada tsakanin mutum-mutumin inji da aka yi a wannan karo, ita ce irinta ta farko a duniya, inda kuma ta zama wani dandali dake yi wa masu kallo a daukacin duniya karin haske game da kimiya da fasaha a wannan bangare. An watsa gasar ga masu kallo na cikin gidan kasar Sin da ketare kai tsaye, matakin da ya ba su damar sanin gajiyar da ake ci daga kimiya da fasaha.
CMG ta gabatarwa al’ummun duniya wata dama mai kyau ta fahimtar kimiyyar mutum-mutumin inji duba da taron mu’ammalar masu kallo da mutum-mutumin inji da ta gudana a ran 1 ga watan nan a cikin gasar kwarewar sana’o’i ta mutum-mutumin inji, zuwa gasa irin ta fada ta wannan karo, har ma da gasar da za ta gudana nan gaba a wannan bangare. Matakin da zai gaggauta bunkasuwar sha’anin zuwa wani sabon mataki na bautawa daukacin al’ummar Bil Adam da amfani da ingantacciyar fasahar zamani. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp