Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)













