Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a Vietnam, shugaban CMG Shen Haixiong, ya kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da shugaban gidan radiyon Vietnam Nguyen Thanh Lam, da shugaban gidan rediyon na Voice of Vietnam Do Tien Sy, kana da shugaban kwalejin yada labarai da fadakarwa na Vietnam Pham Minh Son, a gaban shugabannin kasashen biyu wato Xi Jinping da Tô Lâm. (Amina Xu)