A yau Talata, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, watau CMG, ya fitar da adireshin rassan wuraren da za a yi liyafar bikin bazara na shekarar 2025, baya ga babban muhallin da za gudanar da gagarumin bikin a birnin Beijing.
Rassan sun hada da birnin Chongqing, da birnin Wuhan na lardin Hubei, da birnin Lhasa na jihar Xizang, da kuma birnin Wuxi dake lardin Jiangsu (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)