Yayin da ake bude gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15 a yau Lahadi 9 ga wannan wata, babban rukunin gidajen rediyo da telabijin na kasar Sin wato CMG da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics wato IOC sun daddale yarjejeniyar samun iznin watsa shirye-shiryen wasannin Olympics daga shekarar 2026 zuwa 2032 a birnin Guangzhou dake kasar Sin. Shugaban CMG Shen Haixiong da shugabar kwamitin IOC Kirsty Coventry sun wakilci bangarorin biyu wajen sanya hannu kan yarjejeniyar, kana an gabatar da tambarin CMG na watsa shirye-shiryen gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta Milano Cortina ta shekarar 2026, inda shugaba mai girma na kwamitin IOC Thomas Bach ya halarci taron sanya hannun.
A yayin taron, Shen Haixiong ya bayyana cewa, CMG zai sa kaimi ga raya hadin gwiwa tare da kwamitin IOC a dukkan fannoni, da sada tunanin wasannin Olympics da al’adun gargajiya na kasar Sin ta hanyar watsa shirye-shiryen gasanni da gudanar da bukukuwan wasanni da sauransu, ta haka za a taimaka wajen raya sha’anin wasannin motsa jiki da kiyaye lafiyar jikin jama’a a kasar Sin, kana za a sa kaimi ga bunkasa gasar wasannin Olympics a fadin duniya baki daya.
A nata bangare, madam Coventry ta bayyana cewa, a yayin gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15, sanya hannu kan yarjejeniya a tsakanin kwamitin IOC da CMG yana da babbar ma’ana, kuma batun ya shaida cewa, an bude sabon babi kan raya hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu. Batun ya nuna sada zumunta da yin imani da juna a tsakaninsu, kana ya shaida cewa, bangarorin biyu sun yi kokari tare wajen cika alkawarinsu na sa kaimi ga samun zaman lafiya da hadin kai ta hanyar wasannin motsa jiki. (Zainab Zhang)














