Babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya daddale yarjejeniyar hadin gwiwa da cibiyar musayar al’adun Sin da Girka da kwalejin koyon ilmin wasannin Olympics ta kasa da kasa, don sa kaimi ga musayar al’adu a tsakanin Sin da Girka, da yada tunanin wasannin Olympics tare.
Firaministan kasar Girka Kyriakos Mitsotakis ya taya murnar daddale yarjejeniyar. Kana shugaban CMG Shen Haixiong ya daddale yarjejeniyar tare da shugaban majalisar cibiyar musayar al’adun Sin da Girka na bangaren Girka da shugaban kwalejin koyon ilmin wasannin Olympics ta kasa da kasa.
Mataimakin ministan wasanni na Girka Yannis Vroutsis, ya ruwaito firaminista Kyriakos Mitsotakis na murna da kulla sabuwar dangantakar abota da hadin gwiwa a tsakanin kwalejin koyon ilmin wasannin Olympics na kasa da da kasa da CMG, tare da fatan darajar wasannin Olympics za ta samu ci gaba a zamantakewar al’ummar kasar Sin. (Zainab)