Tun daga ranar 20 ga wannan wata, aka fara gabatar da bidiyon dandanon shagalin murnar Bikin Bazara na kasar Sin a gidajen sinima 78 na manyan birane 5 na kasar Amurka wato New York, da Washington, da San Francisco, da Los Angeles, da kuma Houston, masu kallon kasar Amurka sun jin dadin bikin.
A ranar 23 ga wannan wata kuma, ofishin jakadancin Sin dake kasar Myanmar ya gudanar da shagalin murnar Bikin Bazara na kasar Sin na shekarar 2025, inda aka watsa wannan bidiyon CMG.
- Shugaban Kasar Sin Ya Mika Gaisuwar Sabuwar Shekara Ga Dukkan Jami’an Tsaro
- Gwmana Lawal Ya Bayyana Wa UNICEF Shirin Jihar Zamfara Na Ƙaddamar Da Dokar Kare Al’umma
A ranar 23 ga wannan wata har ila yau, ofishin jakadancin Sin dake kasar Indonesia ya gudanar da liyafar murnar Bikin Bazara na kasar Sin na shekarar 2025, inda aka watsa wannan bidiyo, wannan ne karo na farko da aka watsa bidiyon dandanon shagalin murnar Bikin Bazara na kasar Sin a liyafar, wanda ya kasance wata hanyar fahimtar al’adun bikin ga masu kallo a wurin.
Kazalika, a ranar 25 ga wannan wata, an gabatar da bidiyon a filin Meskel dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha, wanda ya samar da yanayin jin dadin bikin ga yankin gabashin nahiyar Afirka.
Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da bidiyon dandanon bikin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara a Faransa a ran 24 ga watan nan da muke ciki. Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.
Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo.
Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere. Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka.
An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni a shekarar 2024, matakin da ya bayyana cewa, al’adun bikin na kara yaduwa zuwa duk fadin duniya zuwa wani sabon matsayi.