Kamfanin gamayyar kafofin watsa labarai na rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya gabatar da bikin baje shirin bidiyo na musamma a birnin Moscow na kasar Rasha, albarkacin bikin cika shekaru 75 da kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin.
Bikin wanda ya gudana a jiya Talata, ya bayar da damar baje labarai bisa taken “Rubutu a samaniya: Labarina game da kasar Sin”. Kuma shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo yayin bikin.
Cikin jawabin na sa, Shen Haixiong ya ce shirin na bidiyo mai kunshe da labarun ayyukan da CMG ya tattara daga al’ummun kasa da kasa, na kunshe da labarai sama da 1,600 daga abokan kasar Sin na sama da kasashe 60, wadanda ke wakiltar zurfafa dunkulewar yadda al’ummun ke ji a ran su, da kuma mabanbanta al’adu na sassan duniya daban daban. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp