An gudanar da taron karawa juna sani game da aikin watsa shirye-shiryen gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15 ta hanyar talabijin ta zamani, wato taron karawa juna sani na hada fasahohin yada labarai, a jiya Litinin a birnin Guangzhou dake lardin Guangdong na kasar Sin. A yayin taron, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da sabbin manhajoji guda 10 da ya kirkiro ta hanyoyin kimiyya da fasaha don watsa gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15. CMG zai yi amfani da sabbin fasahohi, kamar kirkirarriyar basira ta AI da fasahar tsimin makamashi da kyautata ingancin hotuna da rediyo da dai sauransu, ta yadda zai samar da karin shirye-shirye masu kayatarwa ga masu kallo.
A yayin taron, mamban kwamitin tsara shirye-shirye na CMG Jiang Wenbo ya bayyana cewa, CMG ya ci gaba da zurfafa aikin gina tsarin tsara shirye-shiryen rediyo da bidiyo masu inganci ta dukkanin kafofin watsa labarai. Haka kuma, zai mai da hankali wajen nuna sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ta hanyar nuna shirye-shiryen rediyo da bidiyo masu inganci, da yin amfani da damar watsa manyan bukukuwa da gasanni wajen karfafa aikin yin kirkire-kirkire, ta yadda za a karfafa amfani da fasahar tsara shirye shiryen rediyo da bidiyo masu inganci da fasahar AI cikin aikin watsa gasannin motsa jiki daga wasu kafofi, da kuma inganta fasahohin watsa shirye-shiryen talabijin masu inganci, da aikin tsara shirye-shiryen gasar wasannin motsa jiki. (Mai Fassara: Maryam Yang)














