Babban rukunin gidajen rediyo da telabijin na kasar Sin (CMG) ya gabatar da shirin shagalin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, wato bikin bazara, cikin nasara, tare da nuna wani yanayi na murnar bikin cikin annashuwa ga masu kallo na kasashe daban daban.
An ce, yawan kallon shirin shagalin ta sabbin kafofin watsa labaru da masu kallo na kasar Sin suka yi ya kai wani matsayin bajinta, inda adadin ya kai fiye da sau biliyan 2.8, wanda ya karu da miliyan 690 idan aka kwatanta da jimillar bara.
A nasa bangare, gidan telabijin na CGTN dake karkashin CMG ya yi amfani da harsuna 82 wajen watsa shirin shagalin kai tsaye, da watsa rahotanni game da shi, inda yawan kallon shirin da masu kallo na kasashen waje suka yi ya kai sau miliyan 520. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp