Daga ranar 18 zuwa 21 ga watan nan bisa agogon Rasha, an gudanar da dandalin tattaunawa tattalin arziki na kasa da kasa na St. Petersburg karo na 28 a kasar ta Rasha. Yayin taron, an sake gayyatar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG don halartar dandalin a matsayin abokin huldar yada labarai.
CMG, ya gina wani wurin baje koli mai zaman kansa a cikin wurin taron, da kafa dakin nuna shirye-shirye, da yin hira da manyan baki, kuma ya ba da rahotanni game da dandalin a cikin harsuna da yawa.
Ban da wannan kuma, a yankin baje kolin, an nuna sabon sakamakon aikace-aikacen fasahohin zamani na AI, wanda CMG ya yi nazari da kansa, da gabatar da shirye-shiryen CMG masu inganci da kuma kayayyakin al’adun kasa da kasa da ya kera da kansa, ya kuma jawo hankulan baki ‘yan siyasa da ’yan kasuwa da wakilan kafofin watsa labaru na kasashe daban-daban da suka halarci dandalin, inda suka tsaya tare da ziyartar dakin da ya kafa.(Safiyah Ma)