A ranar 22 ga watan Agustan nan ne aka gudanar da bikin kaddamar da taron tattara ayyukan fina-finai da talabijin da aka samar bisa fasahar AI na duniya mai lakabin “Makoma mai kyau ga Bil’adama” a Hollywood da ke Los Angeles, kasar Amurka. Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da cibiyar nazarin fina-finai ta New York da ke Amurka ne suka shirya taron.
Daraktan CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi a rubuce, inda ya bayyana cewa wannan wani sabon salo ne na amfani da fasahar AI wajen ba da damar kirkiro da fina-finai da shirye-shiryen talabijin, kuma yana fatan matasa a duniya za su yi amfani da fina-finai da shirye-shiryen talabijin a matsayin abokan tafiya, kana fasahar AI ta zama kayan aikin da za su yi amfani da tunaninsu da fikira wajen nuna irin duniyar da za a samu nan gaba ta hanyar fasaha, da mabambantan al’adu, da kuma zaman tare cikin lumana. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp