Yau 29 ga wata, an gudanar da bikin karfafa hadin gwiwa tsakanin babban rukunin gidajen rediyo da talibiji na Sin wato CMG, da mabambantan bangarori na yankin Hong Kong. Jagoran yankin musamman na Hong Kong John Lee Ka-chiu ya bayyana cewa, idan aka waiwayi tarihi, gwamnatin Hong Kong da CMG sun kasance suna hadin gwiwa sosai da juna. Sun yi hadin gwiwa da juna a fannonin ba da rahotannin manyan bukukuwa, da fadakar da al’ummu manufofi masu muhimmanci, da daidaita al’amura na gaggawa. Bikin karfafa hadin gwiwa na yau ya alamanta sabon babin hadin gwiwar CMG da al’ummar Hong Kong. Jerin matakan da aka dauka, ba ma kawai sun dace da manufofin kasa ba, sun kuma amsa bukatun al’ummar Hong Kong, tare da dacewa da burin jama’a na samun kyakkyawar rayuwa.
A lokacin da ake bikin cika shekaru 76 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin, a yau 29 ga Satumba, CMG ta kuma kaddamar da nune-nunen ingantattun shirye-shirye a Hong Kong, inda za a nuna shirye-shirye 9 masu kyau. (Amina Xu)