Yau Litinin 23 ga wata ne, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, da kawancen kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasar Faransa wato LFP, suka daddale wata takardar bayani kan hadin-gwiwa a birnin Paris, inda suka cimma matsaya kan fannonin da suka shafi gudanar da gasanni tare, da kara yin mu’amala, da raya harkokin kwallon kafa na matasa da sauransu.
Mataimakin shugaban sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG, Shen Haixiong, da shugaban kawancen LFP, Vincent Labrune, sun sanya hannu kan takardar bayanin. (Murtala Zhang)ĺ