A jiya Asabar babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya sanya hannu kan takardar fahimtar juna game da hadin gwiwar gudanar da ayyuka, tare da kamfanin Grup Mediapro na kasar Sifaniya, inda sassan biyu suka amince za su rika musayar bayanai a fagen shirye shirye, da fannin tsara shirye shirye, da na amfani da sabbin fasahohin kirkire kirkire, da manhajoji da duniya ke yayi a halin yanzu.
A shekarar 1994 ne aka kafa kamfanin Grup Mediapro a birnin Barcelona, kuma ya zuwa yanzu ya zamo daya daga cikin kafofin watsa shirye shirye mafi karbuwa a dukkanin fadin nahiyar Turai.
Kamfanin na yada shirye shiryensa ga nahiyoyi 5, yana kuma watsa shirye shirye game da wasanni, da shirye shiryen talabijin da na fina-finai. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp