A ranar 24 ga watan Oktoban bana yayin zama na 18 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, an amince da kudurin da ya shafi ayyana ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin, inda aka kebe ranar 25 ga watan Oktoba, a matsayin ranar ta tunawa da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin. Domin tunawa da wannan muhimmin lokaci, CMG wato babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ya gabatar da jerin wasu shirye-shiryen talabijin guda shida bisa wannan take.
Shirye-shiryen sun nuna gaskiyar tarihin da ya shafi yadda Japan ta mamaye yankin Taiwan a shekara ta 1895, har zuwa dawowarsa kasar Sin a shekara ta 1945, inda kwararan shaidu, da maganganun masana da wadanda suka gane wa idanunsu, duk suka bayyana irin zaluncin mulkin mallaka, da tabbatar da cewa, kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan gami da dawowarsa kasar Sin, nasara ce a yakin duniya na biyu, kana, muhimmin bangare na zaman odar kasa da kasa bayan yakin, al’amarin da ya shaida cewa, babu shakka za a samu dinkuwar duk kasar Sin baki daya a nan gaba.
A gun taron manema labarai da ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya, kakakin ofishin, Zhang Han, ta bayyana cewa, tarihi shi ne ya koya mana darasi, kuma muna da yakinin cewa, da mazauna babban yankin kasar Sin da na Taiwan, gami da Sinawa da ke zaune a gida da waje sun kalli shirye-shiryen, ko shakka babu za su tuna tarihi da kiyaye nasarorin da aka samu, da kara kokarin yaki da yunkurin balle yankin Taiwan daga kasar Sin da duk wani shisshigi daga kasashen waje, da ci gaba da taimaka wa babban sha’anin dinke duk kasa baki daya. (Murtala Zhang)














