A ranar 20 ga watan Agustar nan, CMG ya gudanar da bikin baje kolin bidiyo da zane-zane da kuma bikin cudanyar al’adu na “Sautin zaman lafiya” tare da ofishin jakadancin kasar Sin dake Amurka, don tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar Sinawa a kan hare-haren zaluncin kasar Japan, da yaki da ‘yan mulkin danniya na duniya, a birnin Washington na kasar Amurka.
Daraktan CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya bayyana cewa, CMG na son zurfafa hadin gwiwa da abokan huldar kasa da kasa, da isar da sakon muryar kasar Sin wajen nuna adawa da babakeren bangare guda, da ba da shawarar yin adalci, da bin hanyar da ta dace, da fuskantar kalubale ta hanyar hadin kai da hadin gwiwa domin samun ci gaba na bai-daya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)