Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya yi bitar murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin na shekarar 2023 mai taken “Kasar Sin mai wadata a sabon zamani da kara dadin rayuwar al’ummar Sinawa” a karo na farko a jiya Litinin, inda aka nuna kwazo da himman Sinawa masu cike da imani.
Ana ci gaba da nacewa kan manufar kirkire-kirkire yayin da ake shirya murnar bikin bazara na shekarar 2023 dake tafe, inda za a nuna halayyar jarumtaka ta al’ummar Sinawa ‘yan kabilu daban daban ta hanyar samar da shirye-shirye iri iri kamar su wake-wake, da raye-raye, da wasan kwaikwayo da sauransu.
‘Yan wasan fasaha wadanda suka halarci bitar bikin sun yi kokari matuka domin nuna wa masu kallo sabon ci gaban da kasar Sin ta samu a sabon zamanin da ake ciki. Za a yi murnar bikin bazara na shekarar 2023 a ranar 21 ga watan Janairun shekara mai zuwa wato rana ta karshe ta shekarar 2022 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)