Bikin kunna fitilu na gargajiyar kasar Sin, na cikin bukukuwa masu kayatarwa a kasar Sin, kuma a bana, rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin CMG, zai nuna shagulgulan bikin na kunna fitilu da yammacin ranar Lahadi 5 ga watan nan na Fabarairu.
Tuni dai CMG ya tsara kasaitaccen shiri domin bikin, wanda ke kunshe da nune-nune masu salon gargajiyar kasar Sin, ta hanyar wake-waken da can, da wasan kwaikwayo na dandali ko “opera”, da wasannin sarrafa jiki, da wake-wake, da sauran nune-nunen al’adun da aka gada daga kaka da kakanni, masu nuna kyakkyawan yanayin ci gaba da kayatarwar bikin.
Ana tsara nune-nunen kayayyaki masu nasaba da bikin ne bisa kayatattun al’adun bikin na kunna fitilu, wanda aka gada tun kaka da kakanni. Kaza lika yayin bikin, za a nuna fitilun musamman na gargajiyar biranen Beijing, da Qinhuai, da Xiashi, da Chaozhou, wadanda tuni aka sanya su cikin jerin abubuwan tarihi na duniya da aka gada daga kaka da kakanni. (Saminu Alhassan)