Duba da kyawawan manufa, bisa jagorancin cocin Catholic Diocese Yola, ta bada horo kan sana’o’in dogaro da kai ga matasa ‘yan gudun hijira 150, da tallafa musu a Jihar Adamawa.
Babban limamin cocin a jihar, Bishop Stephen Dami Mamza, ya bayyana haka ga ‘yan jaridu a Yola, lokacin da yake raba kayan tallafi ga matasa ‘yan gudun hijiran, da suka fito daga sansanonin Unguwannin Damare, Sangere Dutse, Daware, EYN Wuro Jabbe da Ngurore.
- Yaki Da Ta’addanci: Gwamnatin Tinubu Za Ta Saka Kishin Kasa A Zukatan Al’umma – MinistaÂ
- Tsohon Firaministan Belgium: Ya Dace EU Ta Nuna Matsayar Kanta A Maimakon Kasancewa ‘Yar Koren Amurka
Shugaban ya ci gaba da cewa “matasa ‘yan gudun hijiran da suka samu halartar horo kan sanin halayyar dan Adam (psychosocial) da ilimin ruhini (spiritual), na tsawon watanni 14, muna kuma ba su wani abu duk wata.
“52 daga ciki, mun ba su kudin kayan da za su fara yin sana’a, 27 sun karbi keken dinkin, 71 mun taimaka mu su da naira dubu 100 kowannensu, da za su yi rigista a kwalejojin ilimi da jami’o’i dabam dabam” in ji Dami Mamza.
Bishop Stephen Mamza, ya shawarci matasan da suka amfana da horon da su zama wakilai nagari wajen samar da zaman lafiya, da gudanar da aikin da ya dace da kayayyakin da su ka samu, kamar yadda dama aka tsara.
Madam Helen Ibrahim, daya daga wadanda suka amfana da horon ta gode wa cocin Catholic Diocese Yola, bisa horon da suka samu ta hanyar Mission Take Heart, ba tare da lura da inda ka fito, addini ko kabilar mutum ba.