Tsohon Kocin FC Porto Sergio Conceicao ya maye gurbin Paulo Fonseca a matsayin Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AC Milan bayan da ƙungiyar ta raba gari da Fonseca a daren jiya Lahadi.
Fonseca mai shekaru 51 ya bar Lille domin maye gurbin Pioli a watan Yuni, amma watanni 6 da ya kwashe ya na jagorantar ƙungiyar da ke buga gasar Serie A ta ƙasar Italiya abubuwa basu canza ba kamar yadda mahukuntan suke gani.
- Yau Ake Kece Raini Tsakanin Kungiyoyin Hamayya Na Manchester A Firimiyar Ingila
- Ba Zan Yi Ƙasa A Gwiwa Ba Wajen Ceto Manchester City Ba – Guardiola
Canjaras ɗin da su ka yi a wasansu da Roma da ci 1-1 ya sake ɓata lamarin inda yanzu haka Milan ta ke a matsayi na 8 a kan teburin gasar Serie A, maki 8 tsakaninsu da Atalanta wadda ke jan ragamar teburin.
Sergio Conceicao wanda ya jagoranci FC Porto tsawon shekaru 7 ne ya maye gurbin ɗan ƙasar Portugal ɗin a matsayin Kocin AC Milan wadda zata kara da Juventus a ranar 3 ga watan Janairu na sabuwar shekara.