Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda, ta zama Sakatariyar Gamayyar Ƙungiyar Matan Shugabannin Nijeriya Masu Fafutukar Yaƙi da Cutar Daji (FLAC).
Ƙungiyar tana faɗi-tashi wajen yaƙi da cutar kansa ta ta hanyar wayar da kai, tsara manufofi da kuma shiga tsakani kai-tsaye ga al’umma.
- Jimillar Sayar Da Kayayyakin Masarufi Ta Kasar Sin Za Ta Zarce Yuan Triliyan 50 A Bana
- Mataimakin Shugaban Kamfanin Panasonic: Kamfanonin Sin Dake Samar Da Sassan Kayayyaki Ga Kamfaninsa Sun Kai Dubu 6
Naɗin nata ya nuna matuƙar jajircewa da irin gudunmawar da ta bayar wajen habaka kiwon lafiya, musamman a fannin wayar da kan jama’a game da cutar daji, rigakafin cutar daji da kulawa da masu cutar a Jihar Zamfara da kewaye.
A cikin sabon aikinta na ƙasa, Hajiya Huriyya za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan uwanta mata, matan shugabanni don bunƙasa wayar da kai da tattara kayan aiki don inganta tsarin kula da cutar daji musamman ga al’ummomin da ba su da ƙarfi.
Naɗin nata ya biyo bayan bikin bayar da tallafin cutar daji na FLAC da aka yi a gidan gwamnatin jihar Imo a Asokoro, Abuja, inda suka tattauna kan ƙarfafa ayyukan ceto da inganta yaƙin gano cutar da wuri a faɗin Nijeriya.
Ta hanyar ba da fifiko ga kiwon lafiya al’umma, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bambanta da sauran mata, inda ayyukanta ke amfanar masu rauni kai-tsaye. A ƙarƙashin jagorancinta, Jihar Zamfara ta yi aikin tantance cutar kansar nono kyauta, da wayar da kan jama’a, da kuma ɗaukar cikakken nauyin yi wa masu fama da cutar daji fiye da 100 tiyata. Gudunmawar da ta bayar na Naira Miliyan 3.5 don kula da marasa lafiya masu fama da cutar kansa ya nuna tausayi da kuma yadda ta ke tunkarar ƙalubalen kiwon lafiyar jama’a.
A matsayinta na Sakatariyar FLAC, ana sa ran jagorancinta zai ƙara ci gaba ga ƙungiyar haɗin gwiwar ta ƙasa baki ɗaya, gami da ba da shawarwari ga manufofin kiwon lafiya da suka haɗa da ayyukan hidimta wa al’umma da kulawa da kiwon lafiya. Naɗin nata ya kuma nuna cewa Arewacin Nijeriya na da tasiri kan ayyukan kiwon lafiya gami da cutar kansa.
Taron da aka yi a Abuja ya nuna bayar da tallafin kuɗi ga manyan ƙungiyoyi biyu masu tallafawa cutar kansa da suka haɗa da Network of People Impacted by Cancer in Nigeria (NePICiN) da Health & Psychological Trust Center, wanda ƙara nuna aniyar FLAC na inganta rayuwar masu fama da cutar kansa da waɗanda suka warke.
Shugabar FLAC kuma Uwargidan Gwamnan Jihar Imo, Barista Chioma Hope Uzodimma, ta yaba da shirin a matsayin “babban jari a rayuwa, mutunta rayuwar al’umma da kuma daidaiton kiwon lafiya.”
Taron ya samu halartar wasu fitattun matan manya da suka haɗa da Lami Ahmadu Fintiri (Mataimakiyar Shugabar FLAC), Dr. Linda Ayade, Monica Ugwuanyi, Hajiya Zainab Nasir Idris, H.E. Agyin Kefas, da Hajiya Huriyya Dauda Lawal.
Jajircewar da Hajiya Hariyya ta yi a wannan ƙasa tamu ba wai kawai ya ƙara nuna irin himmarta ba ne wajen fafutukar kula da lafiya har ma ya ƙara ƙarfafa gwiwarta a jihar Zamfara wajen kawo sauyi kan harkokin kiwon lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp