Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) da hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa (NCDC) sun ce, an tabbatar da mutum 7,202 sun kamu da cutar mashako (Diphtheria) a kananan hukumomi 105 kuma cutar ta kashe mutum 453 acikin Watanni goma kacal.
A wata sanarwar hadin guiwa da NPHCDA da NCDC suka fitar a ranar Litinin, sun ce jinkirin samun rigakafi shi ke janyo kamuwa da cutar musamman ga yara ‘yan shekara 5 zuwa 14.
“Sauran jihohin da aka samu kesa-kesan su ne Yobe (640), Katsina (213), Borno (95), Kaduna (16), Jigawa (14), Bauchi (8), Lagos (8), FCT (5), Gombe (5), Osun (3), Sokoto (3), Niger (2), Cross River (1), Enugu (1), Imo (1), Nasarawa (1) sai kuma Zamfara (1).
“Zuwa yanzu, adadin mutune 453 ne aka tabbatar cutar ta kashe,” a cewar sanarwar.
Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate ya kafa kwamitin gaggawa na kasa, duba da yadda cutar ke kara ta’azzara da kuma gano cewa kashi 80 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ba a yi musu allurar rigakafi ba ne.
Tawagar da ke karkashin jagorancin babban daraktan NPHCDA, Dr. Faisal Shuaib da darakta-janar na hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC), Dr. Ifedayo Adetifa, su aka dora wa alhakin tsara ayyukan da za a bi wajen shawo kan cutar da nemo mafita ta yadda za a samar da rigakafi yadda ya kamata.
Daga bisani hukumomin biyu sun bukaci iyaye da su tabbatar da an yi wa ‘ya’yansu rigakafi domin kare su daga kamuwa da cutar.