Kotun koli ta bai wa kananan hukumomin kasar nan ‘yancin cin gashin kansu inda kotun ta yanke hanyar biyan kudaden kasonsu daga gwamnatocin jihohinsu.
Kotun kolin ta bayyana haka ne a wata kara da gwamnatin tarayya ta shigar a kan gwamnatocin jihohi 36 a ranar Alhamis, inda ta umurci gwamnatin tarayya da ta biya kudin kason kananan hukumomi 774 kai tsaye zuwa asusun ajiyarsu.
Wani kwamitin alkalai bakwai, a cikin hukuncin da ya yanke, ya kuma bayyana cewa gwamnatocin jihohi na ci gaba da yin amfani da karfinsu wajen rikewa da kuma amfani da kudaden da aka ware wa kananan hukumomin.
Cikakken bayani daga baya…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp