Da yammacin nan ne muka samu labarin cewa Kwamishinan Kula da Harkokin Addini na Jihar Sokoto, Alhaji Usman Suleiman (Ɗanmadamin Isa) ya rasu.
Kwamishinan dai haziki ne a da ya nuna ƙwazo a dukkan ma’aikatun da ya yi aiki, kamar yadda sanarwar da mai Kwamishinan yada labarai na jihar ta Sokoto, Muhammad Akibu Dalhatu ta bayyana.
Za a yi jana’izarsa gobe da misalin ƙarfe 9 na safe a gidansa da ke yankin Polo Club da ke Sokoto.
Gwamna Aminu Tambuwal ya nuna alhinin rasuwar tare da mika ta’aziyya ga iyalan marigayin da daukacin al’ummar Sokoto.