Alkalin Alkalan Nijeriya (CJN), Mai shari’a Olukayode Ariwoola, ya yi ritaya bayan ya cika shekaru 70 da haihuwa.
An haifi Mai shari’a Ariwoola a ranar 22 ga Agusta 1954.
A ranar 22 ga Nuwamba 2011, aka daga darajar shi zuwa daya daga cikin Alkalan Kotun Koli sannan aka nada shi CJN a ranar 27 ga Yuni 2022.
Ariwoola ya hau kujerar CJN ne biyo bayan murabus din da CJN Tanko Muhammad ya yi.
Majalisar dattawan Nijeriya ta tabbatar da Mai Shari’a Ariwoola a matsayin CJN a ranar 21 ga Satumba, 2022.
Ana sa ran Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun za ta karbi ragamar gudanar da ofishin CJN daga hannun Ariwoola