Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa da LEADERSHIP cewar an dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
Wannan mataki na zuwa ne bayan da majalisar dokokin jihar, ta yi wa dokar da ta ƙirƙiro sabbin masarautu huɗu a lokacin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kwaskwarima tare da rushe su a yau.
- Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokokin Kano Ta Rushe Masarautun Da Ganduje Ya Kirkiro
- Kallo Ya Koma Kano: Gwamna Abba Na Shirin Rattaba Hannu Kan Sabuwar Dokar Masarautar Kano
Sai dai ba a sanar da sake nada Sanusi II a hukumance ba, amma majiyar ta shaida wa LEADERSHIP cewar za a sake nada shi a ranar Juma’a.
A cewar majiyar “Bayan zartar da dokar Sanusi ya dawo kan kujerarsa babu bukatar sanarwa, kawai gwamna ake jira ya tabbatar.”
Tun da farko tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ne, ya yi amfani da dokar wajen tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano na 14 a 2020.
A yau ne dai majalisar dokokin Jihar Kano, ta amince gyaran dokar da ta samar da sabbin masarautu a jihar tare da rushe masarautun da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.
Wannan na zuwa ne bayan zama da majalisar ta yi a yau Alhamis tare da yin duba a kan dokar da ta kirkiro sabbin masarautun.
Zaman majalisar na yau, wanda shi ne zama na uku, majalisar ta amince da kundirin gyaran dokar ta kafa masarautun jihar guda biyar, wanda aka samar a karkashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Tun da fari gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da zai sanya hannu idan majalisar ta amince da gyaran dokar.
Shugaban masu rinjaye kuma wakilin mazabar Dala, Hussein Dala ne, ya gabatar da kudirin gyara dokar a yayin zaman majalisar na ranar Talata.