Rashin wutar lantarki na ci gaba da addabar Nijeriya, bayan babbar layin samar da wutar lantarki na ƙasa ya lalace a yau, Asabar, 11 ga Janairu, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa, wutar lantarki ta fara raguwa daga megawat 2,111.01 da ƙarfe 2 na rana.
Sannan ta sauka zuwa megawat 390.20 da ƙarfe 3 na rana.
Wannan shi ne karo na farko da layin ya lalace a shekarar 2025, bayan kwana 10 kacal da shiga sabuwar shekara.
Haka kuma, wannan shi ne karo na 13 da hakan ya faru cikin watanni 13 da suka gabata.