Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta Nijeriya, NUPRC na duba yiwuwar mayar da wasu muhimman ma’aikatunta zuwa Legas.
Shirin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 14 ga Fabrairu, 2024 wacce kuma Dokta Kelechi Onyekachi Ofoegbu ya sanya wa hannu.
- Nan Da Makonni Uku Ɗalibai Za Su Fara Karɓar Bashi Daga Gwamnatin Nijeriya
- Masana’antar Kera Jiragen Ruwa Ta Sin Ta Samu Karin Riba A Shekarar Bara
Hukumar ta ce, an yanke shawarar ne a kan “bukatar inganta ayyuka hukumar, rage farashin aiki, da kuma yin amfani da kadarorin hukumar da ke Legas”.
Takardar ta kara da cewa, “Dangane da manufofin NUPRC na inganta ayyukanta, haɓaka masana’antu, da rage cunkuso a ofishinta na Abuja, muna duba yiwuwar mayar da wasu rukuni zuwa Legas.
“Wannan yunƙurin ya samo asali ne daga buƙatar haɓaka ayyukanmu, rage farashin aiki, da yin amfani da isassun kadarorinmu a Legas.”
Wannan na zuwa ne makonni kadan bayan manyan rukunin babban bankin Nijeriya, CBN da hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta kasa (FAAN) sun mayar da ofisoshinsu zuwa Legas saboda irin wannan dalili na inganta aikin.