Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauran jami’an tsaro, a ranar Laraba, sun fatattaki ‘yan Boko Haram, da suka kai hari kauyen Bassa-Kukoki, da ke gundumar Allawa a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Majiyoyin tsaron da suka tabbatar wa LEADERSHIP labarin a ranar Alhamis, sun ce, “bayan bayanan sirri da aka samu daga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da suka hada da rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF) da sauran hukumomin tsaro, a 11 ga watan Satumba, 2024 sun yi nasarar fatattakar gungun ‘yan ta’addan Boko Haram da ‘yan bindiga, wadanda suka kai hari kauyen Bassa-Kukoki, gundumar Allawa a karamar hukumar Shiroro, jihar Neja.”
Majiyar ta kara da cewa: “Yayin da aka kashe ‘yan ta’addan da dama, sai dai abin takaici, ‘yan ta’addan yayin da suke tserewa, sun kashe mutane uku da suka gamu a kan hanya, amma babu wani jami’in tsaro da ya rasa ransa a yayin farmakin.”