Wata tankar mai dauke da man fetur ta fashe, inda ta kashe mutane kusan 30 tare da jikkata wasu 40 a hanyar Agaie-Baddegi a jihar Neja.
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa hatsarin ya afku ne a kusa da kauyen Essa, gaba kaɗan da Agaie, cikin Baddegi.
- Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC
- Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya
Wasu majiyoyi daga kauyen da suka shaida faruwar hatsarin, sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Talata.
Sun ce wadanda suka mutu yawancinsu wadanda suka je kwaso man fetur ne a lokacin da tankar ta yi hatsari kafin fashewar.
Shugabannin Direbobin Tankar Mai na Jihar Neja (PTD) da Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NUPENG) ta kasa, Kwamared Farouk Mohammed Kawo, sun tabbatar wa LEADERSHIP faruwar lamarin.