Kocin kungiyar kwallon kafa ta Barau Fc dake buga babbar gasar Firimiya ta Nijeriya Ladan Bosso, ya ajiye aikinsa na horar da kungiyar akan rajin kansa sakamakon wani dalili da ya danganci Iyali kamar yadda kungiyar ta bayyana.
A wani sako da kungiyar ta fitar a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa, “An naɗa Rabi’u Tata a matsayin sabon mai horar da kungiyar Barau FC na rikon ƙwarya bayan tafiyar Ladan Bosso, wanda ya yi murabus saboda dalilan iyali”.
Yanzu haka dai, kungiyar ta Barau Fc na shirye-shiryen tunkarar kungiyar Kano Pillars a wasan Mako na 9 na gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL) a ranar Lahadi.
Sanarwar ta fito ne daga Daraktan yada labarai na kungiyar, Ahmad Hamisu Gwale yau Laraba 5 ga watan Oktoba, 2025.