Majalisar dattawa ta yi karatu na uku a kan gyaran kudirin dokar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA ta shekarar 2024, inda ta amince da hukuncin kisa a matsayin mafi girman hukunci ga masu safarar miyagun kwayoyi a Nijeriya.
Kudirin ya fara aiki ne a ranar Alhamis a lokacin da Majalisar ta yi nazarin diddigi kan kudurin da aka amince da shi a matsayin doka don kiyaye ‘yancin dan Adam da ke tattare da harkokin shari’a.
- Mun Kawo Jam’iyyar AAC Ne Domin Al’ummar Adamawa – Doubli
- NDLEA Ta Kama Wani Fasinja Ɗauke Da Kwayar Tramadol 4,000 A Filin Jirgin Sama Na Legas
Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin shari’a, ‘yancin dan adam da kuma harkokin shari’a, Sanata Tahir Munguno ne ya gabatar da rahoton a gaban zauren majalisar.
Mataimakin shugaban majalisar dattijai wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya yi watsi da kiran da Sanata Oshiomhole ya yi na a sauya hukuncin, yana mai jaddada cewa, kiran ya zo a makare