Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta da suka hada da Sanata da wasu ‘yan majalisar tarayya uku bisa zargin zagon kasa ga jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda ya bayyana rashin jin dadin jam’iyyar da halayyar ‘yan majalisar da aka dakatar.
- NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa
- Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje
‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, da kuma ‘yan majalisar wakilai uku, wato Alhaji Abdullahi Sani Rogo (Mazabar Tarayya ta Rogo), Alhaji Abdullahi Rurum (Mazabar Tarayya ta Rano/Kibiya), da Ali Madakin Gini (Mazabar Tarayya ta Dala).
LEADERSHIP na zargin cewa, daya daga cikin al’amarin da ya jawo dakatarwar shi ne gayyatar da fitattun shugabannin jam’iyyar APC na kasa, da suka hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, suka yi a kwanakin baya, tare da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau, zuwa wani taro da Sanata Sumaila ya shirya. Tarukan sun hada da daurin auren diyarsa da bikin yaye dalibai na farko a jami’ar sa mai zaman kanta dake karamar hukumar Sumaila.
Kasancewar shugabannin jam’iyyar APC a wajen taron, kuma an ki gayyatar ‘ya’yan jam’iyyar NNPP, ya janyo ce-ce-ku-ce a kan yiwuwar komawar Sumaila zuwa APC.
Shugaban NNPP, ya kuma bayyana cewa jam’iyyar za ta kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin tare da daukar matakin da ya dace da su a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp